A cikin wani rahoto da aka fitar, na wata uku a kan harkokin tsaro ya bayyana cewa, an kashe a kalla mutane dubu biyu da ɗari biyar da tamanin da uku 2,583, yayin da aka yi garkuwa da mutane dubu biyu da dari daya da sittin da hudu daga watan Janairu zuwa Mayun 2024.
Rahoton da Jaridar Daily Trust ta wallafa, ya bayyana cewa, Jihohin da abin ya fi tsamari sun hada da Borno da aka kashe mutane 517, sai Benue, mutane 313, Katsina, 252, Zamfara, 212 sai Kaduna 206.
Sai kuma Jihohin da suke a kan gaba wajen yawan mutanen da aka yi garkuwa da su, su ne Kaduna, 546; Zamfara, 447; Borno, 340; Katsina, 252 and the Federal Capital Territory (FCT), 102.
Idan za a iya tunawa, a farkon wannan watan na Afrilu Ministan tsaro na Nijeriya Muhammad Badaru Abubakar da yake jawabi a taron tsaro na kasa karo na farko ya ce, ana samun nasara a kan harkokin tsaro a Nijeriya