Bayan gudanar da Jana’izar marigayi Sarkin Gobir na Gatawa Isa Muhammed Bawa da ‘Yan bindiga suka yi, bayan sun yi garkuwa da shi. A’lummar garin suka fara zanga -zanaga da kone – kone a wasu daga cikin titunan garin.
Matanen sun bukaci gwamnatin Nijeriya kan ta yi bincike ta kuma dyauki matakin hukunta mutanen da suka kashe Sarkin cikin gaggawa.
Masu zanga -zangar sun kai ga kutsawa helkwatar Jami’yyar APC dake yankin tare da fashe-fashe a helkwatar..
Rundunar ‘Yan sanada ta sanar da sanya dokar hana fita a yankin Sabon Birnin dake ƙaramar hukumar sabon Birni a Jihar Sokoto.
Kakakin rundunar Yan sanadan Jihar, ASP Ahmad Rufa’i ya sanar da hakan ya kuma ce, “dokar za ta fara daga ƙarfe shida na safe zuwa shida na yamma 6am/6pm”.
ASP Ahmed ya bayyana cewa ” An ɗauki matakin ne don kare yankin zuwa wani lokaci, sakamakon zanga -zangar da alummar garin suka fara bayan ‘Yan bindiga sun kashe sarkin garin mai martaba sarkin Gobir Alh. Isah Bawa “.