Shugaban riko na karamar hukumar Hin. Adamu Aliyu Wari, ya bada umarnin siyan magunguna domin bayar da daukin gaggawa da kuma bada kariya ga alummar wasu mazabu da ake zargin samun bullar cutar Amai Da Dudawa, domin dakile bazuwar cutar a karamar hukumar baki daya.
Haka zslika Shugaban rikon Karamar hukumar ya kuma dauki nauyin yin aiki da bada magani kyauta ga masu larurar ido sama da 500 Yan asalin Karamar hukumar.
Da yake gabatar da tallafin Hon. Adamu ya tabbatarwa alummar Karamar hukumar cewar a shirye ya ke cigaba da bayar da gudunmawarsa wajen yin duk wani abu da zai samar da cigaban alummar Karamar hukumar kamar yadda ya ke a tsarin gwamnatin kwankwasiyya.