Yaran sun rasu ne, biyo bayan wani rami da suka faɗa da ake zargin wani kamfanin ƙasar Sin da yake gudanar da titin jirgin kasa da zai huce garin Maraɗi na jamhoriyyar Nijar daga Jihar Borno ya ratsa ta garin Kanwa dake Karamar hukumar Madobi ta Jihar Kano.
Dan majalisar Dokoki mai wakiltar ƙaramar hukumar Madobi, Hon. Suleiman Muktar Ishaq, cikin wani Kudiri na gaggawa da ya gabatar a zauren Majalisar, ya buƙaci masu ruwa da tsaki su ja hankalin kamfanonin da suke aikin a Kano, kan su sanya alamomi a duk wani wuri da yake da haɗari, don kaucewa rauni, ko salwantar rayukan Jama’a.
Hon. Muktar, ya ce, “akwai haɗari matuƙa a ramin tunda har yara bakwai suka mutu, kuma akwai makamantansu a wasu wurare.
Sannan ya kuma jaddada cewa, “Idan har Yara bakwai za su faɗa irin wannan rami su mutu lokaci guda, to ina ga Dabbobi kuma ?
Buƙatar Ɗan Majalisar ta sami amincewar ‘yan majalisar da suke neman kamfanin ya yi wani abu na tausayawa game da mutuwar yaran, sannan gwamnati ita ma ta yi Wani abu ga iiyalansu.
Lamarin ya faru ne a garin Hauwa dake mazabar Kanwa a ƙaramar hukumar ta MadobiI, bayan da wani Yaro da shiga cikin ramin da nufin yin wanka da hakan ya zama silar mutuwarsa.
A ƙoƙarin da sauran yaran suka yi na ceto shi, suma suka dinga mutuwa ɗaya bayan ɗaya har su bakwai.