Akalla dalibai 80 suka amfana da tallafin karatu naira dubu hamsin hamsin daga wakilin kananan hukumomin Rano , Kibiya da Bunkure a majalisar Wakilan tarayyar Najeriya *Rt Hon Kabiru Alhassan Rurum*.
Hakan na kunshe cikin labari da maitaimaka masa kan harkokin yada labarai Fatihu Yusuf Abdullahi Bichi ya sanyawa hannu inda yace
An bada tallafin karatun ne ta hannun shugaban kwamitin bayar da tallafin karatu na Dan Majalisa
tsohin shugaban Karamar hukumar Bunkure, Hon. Rabiu Bala.
Da yake bada tallafin, Rabiu Bala yace an baiwa daliban tallafin ne da nufin ne domain rage musu kudin makaranta da kuma taimakawa harkokin karatunsu.
Rabi’u Bala ya ce”Iinna jan hankalinku kan ku mayar da hankali karatun da ku ke yi domin za ku amfana dashi anan gaba.”
Da yake jawabi, Sakataren Kwamitin bayar da tallafin, Alh Dauda Bala Mai Nama Rano, yace *Babban kudurin da Turakin Rano yasa a gaba a wannan zango shine ya Bunkasa harkar Ilmi a kananan hukumomin guda uku da yake wakilta.”
Ya Kuma shaida cewa, “ Hakan ya sanya tun zaman sa wakilin kanana hukumomin a karo na biyu ya himmatu wajen tallafawa daliban dake karatu a Jami’oi da kwalejoji dake Najeriya.”
Ya kara da cewa Turakin Rano, ya gina ajujuwa tare da samarda kayan koyo da koyarwa a makarantun firamare da sakandire dake kananan hukumomin.”
Alh Dauda Me Nama ya ce *Kimanin dalibai 80 kwamitin bada tallafin ya tantance masu karatu a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria sannan kowannensu zai karbi tallafin naira dubu hamsin, inda jimillar kudin ya kai naira miliyan 4.* cewar mai nama
Idan za’a iya ko a kwanakin baya Rt Hon Kabiru Alhassan Rurum ya bada makamancin wannan tallafi ga fiye da dalibai 100 ‘Yan Asalin dake karatu a Jami’ar Bayero ta Kano da Kuma wasu daga cikin daliban dake karatu a kwalejojin Jihar Kano.
Cikin Farin ciki, wasu cikin daliban da suka Amfana da tallafin *Shamsu Saidu Barkum da Rabi’u Ibrahim Kibiya da Abdulhadi Ali Rano da kuma Firdausi Shehu Barde Bunkure* Sun bayyana matukar godiya da jin dadinsu da tallafin karatun da dan majalisar ya basu tare da cewar, Zamu cigaba da yi masa Addu’ar Allah ya kara daga matsayinsa ya Kuma jibanci lamarinsa kamar yadda ya himmatu wajen sauke nauyin al’ummar da yake wakilta.”