Cikin wata takarda da Jaridar “Top Daily News”, ta samu a ranar Juma’a 29 ga watan Disamaba na Shekara 2023 mai lamba No FHC/ABJ/CS/1733/2023 tana ɗauke da ƙunshin sunayen waɗanda ake ƙarar da suka hadar da: gwamnan Jihar Kano da Kwamishinan Shari’a da kuma Babban Akanta na Kano.
Ƙarar an shigar da ita ne gaban Babbar Koton tarayya dake Babban Birin tarayya Abuja a gaban mai shari’a Justice D. U Okorowo .
Maƙasudin shigar da ƙarar shi ne dakatar da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf daga amfani da kuɗin ƙananan hukumomin da ya shirya yi domin gina gadoji a shataletalen ƙofar Ɗan Agundi da Tal’udu.
Kodayake tuni dai gwamnan ya ƙaddamar da fara aikin a yammacin yau Juma’a 29/12/203.
Ana sa ran za a kashe kimanin naira biliyan ashirin da bakwai wajen gina gadojin.