Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ba da izinin sake cigaba da tsarin ciyar da ɗaliban makaranta domin magance ƙalubalen rashin zuwan makaranta ga yara
Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ne ya dakatar da shirin lokacin mulkinsa.
Sai dai a yanzu shugaba Tinubu ya ba da umarnin a farfaɗo da tsarin saboda zai taimaka wajen magance matsalolin da suka shafi ilimi.
BBC Hausa ta rawauto cewar Shugaba Tinubu ya ce idan ba a magance matsalar ba, zai yi matuƙar wahala a iya rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya.
Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana haka a wani taron yini ɗaya da aka yi.
Ministan ya ce an yi taron ne domin samar da hanyoyin aiwatar da dukkanin tsare-tsaren da za su magance duk wani ƙalubale da kuma yadda hukumomi za su taimaka wajen rage matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta