An bukaci al’umar Fulani da su kasance masu riko da kyawawan dabi’un da suka yi shura da su domin ci gaba da rike martabar su ta masu kunya hakuri da hangen nesa a duk inda suke.
Bukatar hakan na kunshe cikin jawabin bayan taro da kungiyar raya al’adun Fulani ta kasa FUDECO, ta shirya da ya gudana a jami’ar jihar Nassarawa da ke Keffi a jihar Nassarawa.
Da yake jawabi, Babban jagoran kungiyar S.S.Nana ya ce “Taron an shirya shine domin dacewa da bikin ranar yan kasa ta duniya da bunkasar ilimin su wanda Majalisar Dinkin Duniya ta ware ake kuma gudanarwa a duk ranar 9 ga wtan Agusta na kowacce shekara.”
Sannan ya ce “A irin wannan rana ana bayyanar da irin martaba da nasarori har ma da kalubalen da al’umomi ke ciki wanda ke zama tarnaki ta fuskar ci gaba da kuma raya al’adu.”
S. S. Nana ya bukaci al’umar fulani da su kasance masu riko da nagartattun halayen da aka sansu da su tin tali-tali, tare da nisantar duk wani abu da zai haifar da koma baya ga ci gaban su da zubar kimar Fulani musamman al’amuran da suka shafi tsaro da rashin zaman lafiya.”
Da yake jawabi a wurin taron, shugaban kungiyar miyetti Allah Kautal Hore, Dr. Abdullahi Bello Bodejo nuna takaici yayi game da yadda wasu cikin ‘ya’yan Fulani ke aro munanan dabi’u da basa cikin al’adun Fulani wanda hakan ke haifar da zubar da kimar Fulani da aka sansu da kunya.
Bodejo ya bada misali da yadda matasan kan yi askin da bai dace ba da Sanya sutturun da suka saba da tarbiyya da shaye shaye da sauran su, inda ya karfafe su da su koma baya domin neman sanin tarihin gishikan abubuwa uku da al’umar fulani suka yi shura akai (Fulako wato Kunya sai Muyal wato hakuri da kuma Hakkilo wato Hangen nesa).
Da ya ke Karin haske game da taron na bana, shugaban kungiyar ta raya al’adun Fulani PUDECO reshen jihar Nassarawa Comrade Muhammad Habib Hussaini, bayyana nasarorin da kunigyar ta FUDECO ta samu yayi, da suka hadar da koyawa matan Fulani sana’o’in dogaro da kai, basu jari, da kuma samar da makarantu a garuruwan na Fulani da sauran su.”
Taron na shekarar 2024 ya samu halartar shugabannin kungiyoyin ci gaban Fulani, da sauran masu ruwa da tsaki, an gudanar da abubuwa masu tarin yawa da suka kunshi gabatar da maqaloli akan muhimmancin dogaro da kai da neman ilimi da tsayuwa akan tsarin tarbiyya da baje kolin al’adu da raye raye da naje kolin sana’o’in Fulani da sauran su.