An buƙaci ma’aikatan dake aiki ƙarƙashin gwamanatin jihar Kano da su yi amfani da ƙarin albashin da gwamnatin Jihar Kano ta yi musu wajen ƙara himma a kan aiki da kuma kyautatawa iyalansu.

Sugaban ma’aikata na Jihar Kano Abdullahi Musa ya yi kiran ne a zantawarsa da manema labarai. Inda ya ce “amfani da kuɗaɗen ta hanyar da ya dace, zai taimaka wajen cimma manufofi da dalilan da suka sanya aka yi karin.

Shugaban mai’aikatan na Kano ya kuma shawarci ma’aikatan da ba sa son zuwa aiki ko zuwa a makare da sutuna cewar, amana ce suka ɗauka cewar, ” za su yi aiki bisa yadda tsarin dokar gudanar da aiki ta ce”

A ƙarshe, ya kuma godewa gwamna Engr Abba Kabir Yusuf bisa yadda ya cika alƙawarin da ya ɗauka na biyan mafi ƙarancin albashin.

Share.

Leave a ReplyCancel reply

Exit mobile version