Majalisar Dokoki ta jahar kano ta karyata wani labari da aka wallafa a shafin wata jarida, dake cewa yan majalisa 23 na jamiyyar NNPP sun mara Gwamna Abba Kabir Yusu, baya kan ya tsaya da kafafun sa, ayin yan majalisar uku ne kadai ke tare da tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso.

A hirar sa da manema labarai a zauren majalisar, shugaban masu rinjaye Hon. Lawan Husaini Dala, yace ‘Ana zargin wasu mutane da ake amfani dasu ake son haifar da baraka da kuma raba tsakanin jagora Rabiu Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf.”

Majalisar Dokokin ta bakin Lawan Husaini Dala, tace Yan majalisar Jamai’yyar NNPP 26, su na nan da biyayyar su ga jagora Kwankwaso da kuma Engr Abba Kabir Yusuf, a matsayin gwamnan kano, don haka masu wannan yunkuri baza su ci nasara ba.”

Share.

Leave a ReplyCancel reply

Exit mobile version